Labarai
Mata ne ginshikin tarbiyar al’umma -Shiekh Usman Bello Torob
Wani malamin addinin musulunci dake nan Kano, Malam Usman Bello Torob, ya ce abu ne mai muhimmanci mata su maida hankali wajen kintsa kansu, don dai-dai-ta yanayin rayuwar al’ummar wannan lokaci da ake ciki, kasancewar su iyayen al’umma.
Malam Usman Bello Torob ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa ta musamman da wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu.
Malamin ya yi kira ga mata musamman na Arewacin kasar nan da su maida hankali wajen cin gajiyar damammaki da ake basu a fannonin rayuwa daban-daban, ta hanyoyin da basu saba tsarin rayuwa da dokokin addinin musulunci.
Malam Usman Torob, ya ce tabarbarewar tarbiyyar mata a zamanin nan ya taimaka wajen lalacewar rayuwar yau da kullum da ake tsaka da fuskanta a yanzu.
KARIN LABARAI
Wata mata ta zargi makociyarta da maita a Kano
Rashin tsaftace baki na kawo bari ga mata masu juna biyu
Uwargida ta gayyaci al’umma shagalin bikin yi mata kishiya
Malamin ya kuma ja hankalin Gwamnati wajen yin dokoki da za su tallafawa rayuwar mata a bangarorin da musulmi ke da rinjaye, don kauda wannan matsaloli da ke yiwa al’ummar wannan zamani barazana.
In da ya buga misali, da yanayin sutura da matan wannan lokaci suka raja’a wajen amfani a ita, a matsayin wani mataki da ke kara angiza mummunar ta’adar fyade da zinace-zinace, da kuma yin koyi da wasu mutane daga yammacin duniya da maza ke yi musamman ma matasa.
Malamin wanda shi ne shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta kasa (FULDAN) na farko, da ya kafa ta da manufar kawo sauyi a rayuwar Fulanin kasar nan baki daya, ya ce akwai bukatar Gwamnati da masu rike a mukaman siyasa da suyi waiwaye tare da yin tunanin makomar wannan al’umma a shekaru kadan masu zuwa, idan basu taimaka wajen dora mata da matasa kan hanya ba.
A karshe Shehin malamin yayi kira ga iyaye da malamai da sauran al’umma da su taka rawar da ta dace, wajen sauke nauyin su na nusar da mata da matasa a kan hanya madaidaiciya.
You must be logged in to post a comment Login