Labarai
Mata ‘yan kasa da shekaru 9 aka fi yiwa Fyade a Najeriya
Cibiyar kula da wadanda suka gamu da Ibtila’in fyade da cin zarafi ta Asibitin kwararru na Murtala Muhammad tace yara mata yan kasa da shekaru 9 ne suka fi fadawa cikin ibtila’in fyade da kuma cin zarafin su a nan Kano.
Sakataren cibiyar kula da wadanda suka gamu da matsalar fyade da cin zarafi mai taken “Waraka” Malam Abba Bello ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Muleka Mugano na nan Freedom Radio wanda ya mayar da hankali kan yadda aikata laifin fyade ke kara ta’azzara a wannan lokaci.
Malam Abba yace cibiyar tana samun bayanai ne daga wajen hukumomin gwamnati daban-daban kan laifukan fyade da cin zarafin mata masu karancin shekaru, don haka akwai bukatar al’umma su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen aikata fyade.
Sakataren Cibiyar Abba Bello yace babban abin takaicin shine yadda mutane ke nunawa wadanda suka gamu da ibitila’in fyade kyara ga tsangwama ba tare da la’akari da irin mayuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki ba, wanda hakan ke jefa rayuwar su cikin mummunan yanayin da ya fi na fyaden.
Malam Abba Bello yayi kira ga iyaye mata da maza musamman manyan mata da suka taba gamuwa da matsalar fyade dasu rika kai rahoto ga Hukumomin tsaro kasancewar shiru da baki da ‘iyaye mata keyi na kara ta’azzara matsalar ta fyade.
You must be logged in to post a comment Login