Labarai
Matasan Arewa sun roƙi majalisa ta gaggauta tantance sabon shugaban EFCC
Ƙungiyar ci gaban matasan Arewacin ƙasar nan ta YANPCE ta nemi majalisar dattijai da ta tantance sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ba tare da ɓata lokaci ba.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Nasiru Musa Jega ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.
Sanarwar ta ce, naɗin Abdurrashid Bawa a matsayin shugaban EFCC abu ne da ya dace kuma hakan zai taimaka wajen daƙile cin hanci da rashawa la’akari da ƙwarewar da yake da ita.
Abdurrashid Bawa ya kuma yabawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan yadda ya bai wa matashin shugabancin hukumar.
You must be logged in to post a comment Login