Labaran Kano
Matasan Kano sun goyi bayan Danjuma Goje kan kin sake tsayawa takara
Inuwar Matasan ‘yan Siyasar jihar Kano mai suna Kano Youth Political Forum ta yi kira ga masu rike da madafun iko a jihar Kano da ma sauran jihohin arewacin kasar nan da su yi koyi da tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya sanata Danjuma Goje kan yunkurin da ya yi kin sake tsayawa takara.
Sanata Danjuma Goje dai ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba saboda a bawa matasa dama su shigo cikin sha’anin gudanar da mulki domin ganin sun kawo canjin da ake bukata.
Kungiyar ta Kano Youths Political Forum ta nuna goyon bayanta kan wannan yunkurin, inda ta bayyana cewa hakan abun a yaba ne duba da yadda yanzu matasa suka fara nunawa sun shirya tsaf domin tunkarar ko wane kalubale ta fuskar shugabanci.
Mataimakin shugaban kungiyar Muhammad Salihu Sagir Takai ne ya bayyana hakan, a wata tattauwana da ya yi da manema labarai a Kano.
Muhammad Salihu Sagir Takai ya ce kasancewar tuni aka sanyawa dokar da ta bawa matasa damar shiga a dama da su a harkokin siyasa, to akwai bukatar wadanda suka dade suna shugabanci su farawa janjewa don bar wa matasa ragamar shugabanci.
A yanzu haka dai Kungiyar wadda ta kunshi ‘ya’yan manyan ‘yan siyasar jihar kano da suka fito daga jam’iyyu daban-daban ta shirya tsaf domin gudanar da gangamin matasan jihar Kano wanda ta sanyawa suna Kano Youths Conference 2019 domin karfafawa matasa guyiwa wajen fitowa a dama da su a harkokin siyasa da sauran al’amuran ci gaban rayuwa.