Labarai
Matatar Dangote ta sake rage farashin man fetur

Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur ga dillalai da kimanin Naira 50 kan kowace lita, bayan faduwar farashin danyen mai a kasuwanar duniya.
A cewar sanarwar da kamfanin ya aike wa abokan hulɗarsa, an rage farashin daga Naira 1,175 zuwa Naira 1,125 kan kowace lita.
Kamfanin ya danganta wannan ragi da sulhun da aka cimma tsakanin Amurka da Iran bayan yakin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya taimaka wajen rage farashin makamashi a duniya.
You must be logged in to post a comment Login