Connect with us

Labarai

Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan man fetur da take samarwa

Published

on

Matatar Dangote ta ƙara yawan fetur da take samarwa zuwa ganga 700,000 a rana

Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan man fetur da take samarwa da kuma rabawa gidajen mai a Najeriya, bayan da ƙarfin tace danyen man da take yi ya kai ganga 700,000 a rana.

Matatar, wadda babban attajirin ɗan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote ya mallaka, ta fara samar da man fetur ne a shekarar 2024, kuma tun daga lokacin take ci gaba da ƙara yawan samar da fetur, dizal, man jiragen sama da sauran kayayyakin man da aka tace.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin isar da fetur zuwa gidajen man da ke haɗin gwiwa da matatar, musamman na MRS, tsakanin ranar Juma’a da safiyar Asabar.

A makon da ya gabata, matatar ta sanar da rage farashin fetur daga naira 1,275 zuwa naira 1,250 kan kowace lita a farashin da take sayarwa ga dillalai, yayin da ta rage farashin dizal daga naira 1,800 zuwa naira 1,700 kan kowace lita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!