Connect with us

Labarai

An kammala shirye-shiryen dawo da mahajjatan jihar kano zuwa gida Najeriya

Published

on

Amirul Hajj na Jihar Kano, Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen dawo da mahajjatan jihar kano zuwa gida Najeriya bayan nasarar kammala aikin Hajjin shekarar 2026.

Amirul Hajj tare da mataimakinsa Alhaji Muhammad Mahraz Karaye da wasu jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano sun kai ziyara ga jami’an kamfanin jiragen saman da za suyi zirga zirgar domin tattauna batutuwan da suka shafi jigilar mahajjatan zuwa Kano.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya ce hukumar na aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa da kuma kamfanonin jiragen sama domin kammala tsara jadawalin dawowar mahajjatan.

Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar da lokacin da za a fara jigilar mahajjatan Kano zuwa gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!