Ƙetare
Matsayar ECOWAS kan juyin mulkin Nijar
Shugabannin kungiyar ECOWAS sun ba da umarnin gaggauta daukar matakin amfani da karfin soji kan gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar.
ECOWAS Sun kuma yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka, AU, da sauransu da su goyi bayan kudurin na kungiyar .
Kungiyar ECOWAS ta ce duk kokarin da aka yi na tattaunawa da gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, shugabannin juyin mulkin sun yi watsi da shi, yayin da suke yin Allah wadai da ci gaba da tsare shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa.
An cimma wannan matsaya ta shugabannin ECOWAS ne a taron koli na musamman kan harkokin siyasa a Jamhuriyar Nijar wanda ya samu halartar shugabannin kasashe takwas da ministocin harkokin wajen kasashen Laberiya da Gambia da aka kammala a Abuja.
Shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani da takwaransa na Burundi, Everiste Ndayishimiye sun halarci taron gaggawa na kungiyar ECOWAS karo na biyu kan Jamhuriyar Nijar bisa gayyatar abokan aikinsu.
You must be logged in to post a comment Login