Kiwon Lafiya
Mazauna garin Jogana sun nemi daukin gwamnatin Kano

Mazauna garin Jogana da ke yankin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano, sun bukaci gwamnati da ta kai musu dauki kan ginin babban asibitin garin da ya tsaya cak inda suka bayyana cewa suna cikin halin matsi matuƙa, kasancewar ba su da wani asibiti a kusa.
Sun ce, rashin asibitin na tilasta su kai marasa lafiya har zuwa Babban Asibitin Sir Sunusi da ke Yan Kaba yankin karamar hukumar Nassarawa, abin da ke jefa su cikin ƙalubale da wahalhalu musamman a lokacin bukatar gaggawa.
Mutanen garin sun bayyana hakan ne lokacin da suka kai koken nasu zuwa Sakatariyar karamar hukumar domin kai koken su ga shugaban karamar hukumar.
Da ya ke jawabi yayin ziyarar, Mukaddas Bala Jogana, wanda ya samu wakilcin Kansilan mazabar Jogana, Yusif Isma’il, ya bukaci mutanen da su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar musu da cewa aikin ginin asibitin zai ci gaba ba tare da wata tangarda ba.
Mazauna garin na Jogana dai, sun yi fatan gwamnatin jihar Kano za ta ɗauki matakan gaggawa wajen ganin an kammala aikin asibitin, domin a kawo ƙarshen wahalhalun da suke fuskanta wajen neman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login