Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Me ya sa malaman jamia ke son Jima’i da dalibai?

Published

on

Manyan makarantun Najeriya da sauran jamioi na fuskantar matsalar cin zarafi a hannun malaman jamia da sauran manyan makarantu na kasar nan.

A yan shekarun baya ake ganin matsalar ta ta’azzara a tsakanin malaman na manyan makarantu, tun ana tsegumi akan dalilan da ya saka manyan malaman jamio’in ke neman daliban su, sai ga abubuwa suna fitowa fili ta hanyar binciken kwakwaf da kafafan yada labarai suke yi akai.

Wasu lokutan daliban ne ke fitowa a fili su fadawa  Duniya cewa malaman na manayan makarantun na neman su ammma ana karyatawa.

Hakan ce ta saka kafafafan yada labarai suka fito da labaran binciken kwakwaf na gano yadda malaman jamiar ke cin zarafin dalibai da yadda suke yi musu alkawarin ciyar da su jarrabawa idan har sun yi amfani da su.

Irin wadannan zarge zarge bai tsaya a nan ba ,ana ganin ba malaman jamio’i ba, har malaman makarantun Addinai suna fadawa irin wannan koma ta cin zarafi ko lalata daliban su mata ,ta hanyar bin su ta lallama ko ta yin barazanar fadar da su jarrabawa idan har basu bayar da kan su ba .

Yayin da Duniya take dada dawowa tafin hannu ,irin wadannan matsaloli na cin zarafi sun fara bayyana, ta amafani da daukar hotuna ta Bidiyo da yake bayyana irin zargin da ake yi wa malaman manyan makarantun Najeriya.

Ko a watan Yunin shekarar 2018 sai da jamiar Obafemi Awolowo ta kori wani babban malami Richard Akindle sakamakon neman ya sadu da dalibar sa,mai suna Monica Osagie.

A wancan lokaci Monica Osagie ta bayyana cewa Farfesa Richard Akindele ya nemi da ya santa a matsayin ta na mace sannan ya kara mata maki, a jarrabawar da zata rubuta.

Sakamakon neman daliba Monica Osagie da Farfesa Akindele yayi ,ta saka jamiar Obafemi Awolowo ta kori malamin jamiar sakamakon cin zarafin dalibar ta sa.

An dai kama tsohon malamin jamiar sakamakon tattaunawa da aka kama shi yayi ta hanyar daukar hirar su da aka yi ta naurar daukar murya.

Daga bisani jamiar Obafemi Awolowo  ta kafa kwamitin bincike a jamiar sannan ta kori tsohon Farfesa sakamakon samun sa ,da aka yi dumu dumu da neman dalibar sa Monica Osagie.

A dai watan Yunin shekarar 2018 Farfesa Eyitope Ogunbodede wanda shi ne shugaban jamiar Obafemi Awolowo ya bayyana korar tsohon shehin malami Richard Akindele.

Cin zarafin dalibai mata a jamio’in na Najeriya ana ganin, korar Farfesa Richard Akindele bai canja zani ba wanda sai gashi wani faifan bidiyo da ake zargin wani malamin jamiar Legas Dr Boniface na kokarin haikewa wata mai daukar rahotan binciken kwakwaf ta kafar yada labarai ta BBC.

Faifan bidiyan da kafar yada labaran ta BBC ta fitar ya nuna Dr Boniface na tattaunawa da yar jaridar da ta bayyana a matsayin daliba, a yanzu ita ma jamiar ta Legas ta dakatar da farfesan da rufe ofishin sa.

Ko ta ta yaya manyan makarantun Najeriya zasu fara gyara.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!