Labarai
Minista Ata ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar Galadiman Abbas Sunusi

Ministan gidaje da raya birane Alhaji Yusuf Abdullahi ATA, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi.
Ministan ta cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministan, na musamman kan harkokin yada labarai Adamu Aminu, ya fitar, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da masarautar Kano har ma da al’ummar jihar nan baki daya bisa babban rashin.
Haka kuma, ta cikin sanarwar, Ministan, ya bayyana marigayi Alhaji Abbas Sunusi a matsayin mutumin da ya taka muhimmiyar rawa a tarihin jihar Kano musamman ma kasancewarsa mafi tsufa kuma guda cikin masu nada sarki.
You must be logged in to post a comment Login