Kiwon Lafiya
Ministan cikin gida ya gana da shugabannin jami’an tsaro don magance rikicin makiyaya a jihar Filato
Ministan cikin gida Janal Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya gana da shugabannin jami’an tsaro sakamakon rikicin da ya kunno kai a jihar Filato na kashe makiyaya.
Dambazau ya bayyana haka ne ga manema labarai kammala taron inda ya nuna damuwar sa matuka gamida tashin hankalin.
Dambazau ya kara da cewa rikicin jihar Benue na bukatar a hada hannun don kawo karshen.
Taron dai ya samu hallaratar Hukumar shige da fice da rundunar ‘Yansanda kasa da hukumar tsaro ta Civil Defence da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da Rundunar Tsaro na farin kaya da takwarasa na liken asiri da hukumar fasa kauri ta kasa da kuma hukumar ci gaban al’umma na majalisar Dinkin Duniya.