Kiwon Lafiya
Ministan harkokin cikin gida ya bayyana takaici yadda ya tsinci tarin kalubalen a yayin aiki da tsohon sufeton janar ‘yan sanda
Ministan harkokin cikin Gida Laftanal janar Abdurraham Dambazau ya bayyana takaicin sa kan yadda ya tsinci tarin kalubale lokacin da yake aiki da tsohon sufeto janar na ‘yan’sandan kasar nan Ibrahim Kpokun Idris lokacin yana bakin aikin sa.
Danbazau ya bayyana hakan ne jiya lokacin lokacin da ya ke karbar bakuncin sabon Sufeton yan’sandan Mohammad Adamu a birnin tarayya Abuja.
Ya kuma ce, yana fatan Sabon Sufeton ‘yan’sandan Muhammad Adamu ba zai yi koyi da irin dabi’un tsohon sufeton ‘yan’sandan kasar nan ba, a cewar sa a shirye ya ke don ganin sun bashi gudunmawa wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.
Laftanar janar Dambazau ya ce a wannan lokacin za suyi kokari don dawo da dangantar dake tsakaninsu da rundunar yan’sanda kasar nan don yin aiki kafada da kafada da hukumin tsaro kamar yadda yake fuskantar matsalar tsaron a fadin kasar nan.
Da yake jawabi sabon Sufeton ‘yan’sandan Muhammad Adamu yayi alkawarin canja yadda yake gudanar da aikin sa tare da kawo gyara akan harkokin tsaron kasar nan.