Labarai
Ministar kudi ta bukaci karfafa bankin raya kasashen Afrika
Ministar kudi Kemi Adeosun ta bukaci da a kara karfafa bankin raya kasashen afurka AFDB domin ya iya biyan bukatun kasashe mambobin sa.
Mrs Adeosun ta bayyana hakan ne yayin ganawarta da shugaban bankin Akinwumi Adesina da gwamnonin bankin da kuma ministocin kudade na yankin yammaci da tsakiyar afurka wanda aka gudanar a shalkwatar bankin da ke birnin Abidjan babban birnin kasar Cote d’Ivoire.
Kemi Adeosun ta ce tun da yake manufar kafa bankin ita ce taimakawa kasashen afurka ta bangaren bunkasa tattalin arzikinsu a don haka ba daidai bane a yi watsi da wannan dama.
Ministar ta kuma ce kasar nan ta fuskanci matsalar koma bayan tattalin arziki a ‘yan shekarun nan sakamakon faduwar farashin man fetur, a don haka ta bukaci bankin da ya tallafa wajen farfado da komadar tattalin arzikin kasar nan da ke dada samun tagomashi a wannan lokaci.
Wannan dai shi ne karon farko da bankin ya gudanar da irin wannan taron tun bayan kafashi a alif dari tara da sittin da uku.