Labarai
Ministocin ilimi na kungiyar D8 zasu karfafa shirin inganta kiwon lafiya
Ministocin ilimi na kungiyar kasashen D8 ciki har da Najeriya sun yanke shawarar karfafa shirinta na aiwatar da tsarin kiwon lafiya da karfafa al’umma.
Kungiyar ta D8 wadda kuma ta maida hankali ga fannin kiwon lafiya da tattalin arziki, ta sanar da hakan ne bayan kammala taronta a karon a farko na tuntubar juna a Abuja.
Kasashen da ke cikin kungiyar sun hadar da Bangladesh da Egypt da Indonesia da kuma Iran. Sauran su ne Malaysia da Pakistan da Turkiyya, sai kuma Najeriya.
Babban jami’in kungiyar Dokta Ado Muhammad, wanda kuma shi ne tsohon babban daraktan hukumar kula kiwon lafiya a matakin farko ta tarayya, ya shaida cewa sun samar da wannan tsari na kyautatawa al’umma a cikin watan Nuwamban bara, bayan cimma matsaya kan abinda ya shafi bunkasa harkokin kiwon lafiyar al’umma.