Labaran Wasanni
Moffi da Zaidu za su kara da Stuttgart a Europa League

Fitattun ‘yan wasan Super Eagles, Terem Moffi da Zaidu Sanusi, za su jagoranci FC Porto a wasannin zagaye na 16 na UEFA Europa League, inda za su fafata da VfB Stuttgart ta Jamus.
Ana sa ran ‘yan wasan biyu za su taka muhimmiyar rawa yayin da Porto ke neman zurfafa tafiya a gasar Turai.
A daya bangaren kuma, Ola Aina da kungiyarsa Nottingham Forest za su karbi bakuncin FC Midtjylland ta Denmark a wasan farko, kafin a buga wasa na biyu ranar 19 ga Maris.
Idan Forest da Aston Villa suka tsallake, akwai yiwuwar haduwar kungiyoyin biyu na Premier League a zagayen kwata fainal, yayin da Villa za ta kara da Lille OSC.
Za a buga wasannin farko ranar 12 ga Maris, yayin da na biyu za su gudana ranar 19 ga Maris.
You must be logged in to post a comment Login