Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wata kila Chukwueze ba zai bugawa Najeriya wasa ba

Published

on

Dan wasa Najeriya dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Villarreal Samuel Chukwueze zai fara daukar matsakaicin horo a ranar bakwai ga watan Maris bayan kammala yi masa aiki sakamakon rauni da ya samu.

Chukwueze ka iya rasa wasannin da Najeriya zata kara da Benin Republic da kuma Lesotho a wasannin share fagen gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2021 da za a gudanar a ranar 22 da 30 ga watan Maris.

Kwararran likita Dakta Ulrike Muschaweck ne ya yiwa Chukwueze aikin a birnin Munich dake a kasar Jamus.

Rahotanni na cewa rashin Chukwueze a wasannin ka iya kawowa Najeriya tasgaro yayin da take neman a kalla maki uku a wasannin guda biyu.

Chukwueze dai ya yi nasarar cin kwallo biyu tare da taimakawa wajen cin guda biyar a wasanni ashirin da biyu da ya bugawa Villarreal a wannan kakar wasan da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!