Manyan Labarai
Annobar Corona ba ta tsayar da ayyukan mu ba – NITDA
Shugaban hukumar bunkasa fasahar zamani ta kasa wato NITDA Kashifu Inuwa Abdullahi ya bayyana cewa duk irin yadda annobar corona ta shafi al’amura da yawa amma bata tsayar da ayyukan hukumar tasa ba.
Kashifu Inuwa Abdullahi ya bayyana haka ne ta cikin shirin Barka da Hantsi na tashar freedom Rediyo da aka gudanar ta kafar Internet.
Shugaban yace maimakon tsayar da ayyukan nata sai ma amfani da fasahar sadarwa da tayi wajen wayar da akan mutan dangane da cutar tare da bunkasa tattalin arzikin kasar nan, inda yace hukumar na kokari don ganin kasar nan ta yi kafada da kafada da sauran kasashe a bangaren fasahar sadarwa.
Ya ce, NITDA na kokari sosai don ganin jama’a a arewan kasar nan na amfani da kafar sadarwa don saukaka musu gudanar da al’amuran su na yau da kullum.
Barka da hantsi na yau dai, wanda ya mayar da hankali kan tasirin da fasahar sadarwa ta yi na bunkasa tattalin arziki, a yayin da ake fama da cutar corona da ta haddasa matsalar tattalin arziki a duniya baki daya.
You must be logged in to post a comment Login