Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mu yi amfani da bikin Sallah wajen yi wa ƙasa addu’a- Jibril Falgore

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci al’umma da su yi amfani da wannan lokaci na bikin Sallah wajen yi wa jiha da ma ƙasar nan addu’ar samun sauƙi daga halin da take ciki tare da nuna kyautayi da jin ƙai ga sauran al’umma.

Shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ne ya buƙaci hakan ta cikin saƙonsa na barka da Sallah ga al’ummar musulmi wanda Sakataren yaɗa labaran majalisar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar.

Sanarwar ta ruwaito cewa, shugaban majalisar ya kuma taya al’ummar musulmi murnar zagayowar bikin Sallar bana tare da fatan kammala shagulgula lafiya.

Haka kuma shugaban majalisar, ya buƙaci al’umma da su kasance masu gudanar da kyawawan ɗabi’u musamman bisa koyarwar addinin Musulunci da Manzon tsira.

Shugaban majalisar dokokin ta jihar Kano, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ta cikin sanarwar, ya kuma sha alwashin ci gaba da gudanar da jagorancin majalisar yadda ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!