Labarai
Sarki Muhammadu Sanusi II ya buƙaci gwamnatin Kano ta ci gaba da ayyukan alheri

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci gwamnatin jihar kano da ta ci gaba da yin ayyukan alheri da ta ke wa al’umma na raya birni da karkara.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin daya kawowa mai Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ziyara barka da sallah tare da dukkanin hakimansa a fadar gwamnatin Kano.
Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya ce, dole ne gwamna ya tashi tsaye a kan wasu mutane da basason cigaban Kano daya dauki mataki a kansu don samun kwanciyar hankali al’ummar jihar Kano dama ƙasa baki daya.
Hala kuma, ya godewa gwamnatin jihar Kano Musamman yanda aka bawa bangaren ilimi fifiko da lafiya da kuma yanda ake gyare gyaran hanyoyi da taimakawa al’umma musamman na karkara.
Sarkin ya bukaci gwamnatin Kano data saurari yan kasuwa da suka rubuta abubuwan da suke da bukatar za’a ayiwa kano da kuma fatan gwamnatin kano za tayi musu jagoranci zuwa gwamnatin tarayya domin kano itace cibiyar kasuwan.
Sarkin ya kuma yi wa shugaba Tinubu barka da Sallah da kuma yin fatan gwamnatin tarayya za ta shigo jihar Kano domin yin muhimman ayyuka masu yawa.
You must be logged in to post a comment Login