Labarai
Muhimman bayanai game da Malam Aminu Kano bayan cikarsa shekaru 42 da rasuwa

An haifi Malam Aminu Kano a shekarar 1920 a birnin Kano. Mahaifinsa, Mallam Yusufu, malami ne a fadar Sarkin Kano. Aminu Kano ya tashi cikin kulawa da ilimin addini da na zamani. Ya fara karatu a Shahuci Elementary School, sannan ya ci gaba a Katsina Training College, Daga nan ya samu tallafin karatu zuwa kasar Ingila a shekarar 1946.
Malam Aminu Kano ya fara aiki a matsayin malami, amma ya fi shahara wajen bayyana ra’ayinsa kan danniya da rashin adalci da ake yi wa talakawa a lokacin mulkin mallaka. Wannan ne ya jawo shi cikin harkokin siyasa da fafutukar kawo sauyi.
A shekarar 1950, ya kafa jam’iyyar NEPU (Northern Elements Progressive Union) wacce ta yi tashe a Arewacin Najeriya. Daga baya kuma, ya kafa jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) a 1978, wacce ta yi fice da manufofinta na kare marasa galihu tare da ganin an tabbatar da gaskiya.
Marigayi Malam Aminu Kano yana daya daga cikin ‘yan siyasar farko da suka tsaya tsayin daka wajen kare hakkin mata da kuma ganin an bai wa kowa dama cikin al’umma. Ya kasance yana kira da a ba mata dama su yi ilimi, su fito siyasa, kuma a rushe tsarin da ke danne su.
Marigayin ya rasu a ranar 17 ga Afrilu, 1983. Bayan rasuwarsa, an ci gaba da karrama shi ta hanyoyi daban-daban. A yau akwai wurare da dama da ke dauke da sunansa kamar su, Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, da kwalejin Aminu Kano Islamic and Legal Studies, da kuma titin Aminu Kano Crescent a birnin Abuja.
A koda yaushe marigayin bashi da wani sako ga al’umma da ya wuce adalci, gaskiya da kishin kasa ba.
Marigayin Malam Aminu Kano, ba wai dan siyasa bane kawai, a’a ya kasance muryar talakawa, wanda har yanzu kalmominsa na tasiri tare da haskakawa ‘yan siyasa da masu kishin kasa hanya.
Kazalika ya kasance mutum mai jajircewa da son kawo sauyi da kuma sadaukarwa, a yau Alhamis ne marigayin ke cika shekaru 42 da komawa ga mahaliccinsa.
You must be logged in to post a comment Login