Connect with us

Labarai

Mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba – Gwamna Abba

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yawan al’ummarta da kuma kasancewarta jiha mai ɗauke da mutane daga sassa daban-daban na Najeriya. 

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ambasada Ibrahim Waiya, wanda ya wakilce shi a taron farko na shekara-shekara kan tsaro na Institute of Security and Strategic Studies, inda aka bai wa gwamnan lambar yabo kan kyakkyawan shugabanci a harkokin tsaro.

 

Ya ce Kano ta yi kama da “ƙaramar Najeriya” saboda yawan jama’a da kuma yadda mutane daga sassa daban-daban na ƙasar ke zaune a jihar.

 

 Gwamnan ya kuma bayyana matakan da gwamnatinsa ke ɗauka wajen inganta tsaro, ciki har da horar da matasa kusan 2,000 ƙarƙashin Neighbourhood Watch da tura su ƙananan hukumomi 44 domin taimakawa jami’an tsaro.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!