Connect with us

Labarai

An gano gurneti a cikin magudanar ruwa a Maiduguri

Published

on

Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta ce jami’anta sun gano wani gurneti a kan wani murfin magudanar ruwa a yankin Moduganari da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Rundunar ta ce jami’an sashen EOD-CBRN Base 13 ne suka kwashe gurnetin bayan samun rahoton abin da ake zargin wata na’ura ce mai fashewa da misalin ƙarfe 12:40 na rana ranar Asabar.

Kakakin rundunar, Nahum Daso, ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Naziru Abdulmajid, ne ya bayar da umarnin a tura jami’an zuwa wurin bayan samun rahoton.

Ya ce jami’an sun isa wurin cikin gaggawa tare da kwashe gurnetin ba tare da ya fashe ba. An kuma adana shi domin gudanar da ƙarin bincike.

Rundunar ta ce tana gudanar da bincike domin gano inda gurnetin ya fito da kuma yadda ya isa wurin da aka gano shi.

’Yan sandan sun yabawa mazauna yankin da suka sanar da su lamarin cikin gaggawa, tare da gargadin jama’a da kada su taɓa, ɗauka ko motsa duk wani abu da suke zargin na’urar fashewa ce.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!