Connect with us

Labarai

Rundunar Soji sun lalata sansanonin kungiyar IPOB guda uku

Published

on

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun lalata sansanonin kungiyar IPOB guda uku tare da kwato makamai da abubuwan fashewa a jihar Anambra.

 

Ta cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta, Rundunar ta ce samamen ya faru ne da sanyin safiyar jiya Asabar a Osuakwa, da ke kan iyakar kananan hukumomin Ihiala da Ogbaru, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan mutanen da ake zargi mambobin kungiyar ne.

 

A cewar rundunar, dakarun da ke karkashin Operation UDO KA sun yi arangama da wadanda ake zargin mambobin IPOB ne, inda aka kashe mutum uku. 

 

Sojojin sun bayyana samamen a matsayin babban koma-baya ga masu aikata laifuka da ke neman kawo cikas ga zaman lafiya a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!