Labaran Wasanni
Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich
Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Thomas Muller, ya sake sabunta yarjejeniyar kwantiragin cigaba da wakiltar kungiyar na shekaru uku zuwa shekarar 2023.
Mai shekaru 30, Muller wanda ya fara wakiltar kungiyar ta Bayern a shekarar 2008, ya kara kwantiragin nasa da zai tsawaita shekarun sa da za su haura shekar 15, yanzu haka da ya shafe a kungiyar.
A baya dai dan wasan, ya nuna aniyar sa ta shirin barin kungiyar a watan Janairu, wanda hakan ya kawo rade radin na cewar zaman dan wasa a kungiyar ya kare, da kungiyoyi irin su Totenham, Manchester United da Juventus da Inter Milan, suka nuna sha’a war daukar dan wasa.
Sai dai yanzu haka saka hannu akan kwantiragin da dan wasan ya yi, ya kawo karshen rade radin da ake na barin sa kungiyar, wanda a yanzu haka dan wasan ya buga wasa sama da 500, ga kungiyar ta Bayern, ya kuma zura kwallo goma a gasar kakar wasa ta bana kafin ta samu tsaiko da bada taimako wajen zura kwallo sau 18.
Labarai masu alaka.
Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni
Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana
Shugaban kungiyar ta Bayern Munich, Karl Heinz Rummeniegge, da daraktan wasanni Hasan Salihamidizic, sun bayyana jin da din su da yabawa dan wasan da hazakar sa a cikin filin wasa.
Thomas Muller, ya dau kofin duniya a shekarar 2014 da aka kammala a kasar Brazil, ya kuma lashe gasar champions league a shekara ta 2013, tare daukar gasar Bundesliga ta kasar Jamus, sau takwas da lashe gasar kofin kalubale na kasar mai taken DFB Pokal har sau biyar, sai gasar kungiyoyin nahiyoyi ta world club cup sau daya.
Zuwa yanzu haka dai kungiyar Bayern, ke kan gaba a gasar ta Bundesliga da maki 55, bayan zagayen wasanni 25 inda ta bada tazarar maki hudu ga mai biye mata kungiyar Dortmund, kafin a dakatar da gasar sakamakon Corona Virus.
You must be logged in to post a comment Login