Connect with us

Labaran Wasanni

Mun amince da sabon canjin ‘yan wasa a fili – LMC

Published

on

Kamfanin shirya gasar cin kofin kwararru ta Najeriya wato LMC ya tabbatar da amincewa da yin canjin ‘yan wasan sau biyar yayin gudanar da gasar NPFL a kakar wasa ta 2020/2021.

A dai farkon watan Oktoba da muke ciki ne hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta bada damar dawowa ci gaba da gasar ta NPFL ranar 15 ga watan Nuwamba bayan da aka dakatar da wasanni tsawon watanni 8 sakamakon cutar COVID-19.

LMC: An saka sharuda ga kungiyoyi a kan dawowa gasar

LMC za ta wayar da kan kungiyoyi a kan lasisi

Shugaban kamfanin na LMC Shehu Dikko ya ce a kowane lokaci dan wasa ka iya samun rauni duba da yadda aka dade ba tare da yin wasanni ba, hakan ne ya saka aka bada damar yin canji har sau biyar ga kowace kungiya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!