Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

CAF: Dan kasar Kenya ne zai busa wasan Najeriya da Sierra Leone

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta zabi dan kasar Kenya Peter Kamaku a matsayin alkalin wasa da zai jagoranci wasan Najeriya da Sierra Leone a neman tikitin gasar cin kofin Afirka da za a yi a wata mai kamawa.

Super Eagles za ta hadu da Leone Stars a wasan farko da za a gudanar a filin wasa na Samuel Ogbemudia na birnin Benin dake jihar Edo a watan Nuwamba mai zuwa.

Kamaku ne zai jagoranci alkalancin wasan yayin da Gilbert Kipkoech Cheruiyot da Tony Mudanyi Kidiya da kuma Anthony Juma Ogwayo za su taimaka masa wajen kula da alkalancin wasan.

Najeriya dai na kan gaba a rukunin L da maki 6 bayan da ta yi nasara kan kasar Benin da Lesotho a shekara ta 2019, yayin da Sierra Leone ta kasance a baya cikin rukunin inda ta yi rashin nasara a wasan ta biyu na farko.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!