Labarai
An bai wa jami’an KAROTA mata damar sanya Hijabi
Hukumar lura da zirga-zirgar ababen haa ta jihar Kano KAROTA ta amince jami’anta mata su rika sanya Hijabi yayin gudanar da ayyukansu.
Wannan dai ya biyo bayan korafi da wasu jami’an hukumar mata suka yi a kwanakin baya kan rashin basu dama su rika sanya Hijabi a bakin aiki.
Matan da ke aiki a hukumar ta KAROTA dai a zantawarsu da freedom radio a waccan lokaci, sun ce sun yi iya kokarinsu don ganin an basu dama su rika sanya hijabi, amma hakan ya ci tura.
Saboda haka ya sanya freedom radio ta tuntubi hukumar KAROTA kan wannan batu inda mai magana da yawun hukumar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya bayyana matsayar hukumar kan wannan lamari.
‘‘Hukumar KAROTA a ko da yaushe tana iya kokarinta wajen ganin ta janyo hankalin mata da su shiga aikin ana damawa da su’’.
‘‘Kuma babu wani lokaci da muka ce mata su daina sanya hijabi’’ a cewar Nabulusi Kofar Na’sa’’
You must be logged in to post a comment Login