Labarai
Mun bude wa PFIPC asusun ajiyar kudaden kasashen waje guda biyu- CBN

Babban bankin Najeriya CBN, ya bayyana cewa ya bude wa hukumar da ake takaddama kan sahihancinta mai suna ‘Presidential Foreign Investment Promotion Council’ PFIPC asusun ajiyar kudaden kasashen waje guda biyu.
CBN ya bayyana hakan ne a zaman da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai karkashin jagorancin Yusuf Gagdi ya gudanar, domin bincike kan hukumar.
Daraktan sashen ayyukan banki na CBN Hamisu Ibrahim wanda ya wakilci bankin a zaman, ya ce an bude asusun biyu ne bayan samun umarni daga ofishin akanta janar na tarayya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce daya daga cikin asusun na Dalar Amurka ne, yayin da dayan kuma na Fam din Birtaniya ne.
Hakan na zuwa ne yayin da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya gurfana a shalkwatar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, domin bayar da shaida a binciken da ake yi kan ayyukan wannan hukuma da ake zargin ba ta da sahihanci.
You must be logged in to post a comment Login