Labaran Kano
NAPTIP ta cafke tsohon da ake zargi da yin lalata da kananan yara a Kano
Hukumar yaƙi da safara bil’adama ta ƙasa NAPTIP ta tabbatar da cafke wani tsoho ɗan kimanin shekaru 54 da ake zargi da lalata wasu ƙananan yara a Kano.
Shugaban hukumar na ƙasa reshen jihar Kano Shehu Umar ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio a yammacin yau Talata.
Hukumar na zargin tsohon mai suna Baba Alhaji dake yankin unguwar Ƙulƙul a karamar hukumar Dala da ke birnin Kano da yin fyaɗe ga wasu yara mata ƙanana masu shekaru 12 zuwa 13.
Mutumin da ya jagoranci bankaɗo wannan ta’asa da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Freedom Radio cewa, sun samu rahoton, Baba Alhaji wanda dillalin filaye ne, yana aikata baɗala da ƙananan yara a wani kango dake unguwar Bajallaɓe a yankin ƙaramar hukumar Ungogo.
Daga nan ne kuma jama’ar unguwar suka yi haɗaka har ta kai sun damƙe tsohon tare da miƙashi ga hannun hukuma.
You must be logged in to post a comment Login