Labarai
Mun ceto ‘yan mata da aka yi safarar su zuwa Lebanon – NEMA
Gwamnatin tarayya ta ce ta ceto wasu ‘yan mata ‘yan najeriya su 71 daga kasar Lebanon wadanda faifan bidiyon su ya rika yawo a kafafen sada zumunta suna kuka tare da neman taimako.
Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA Bitrus Samuel wanda ya fitar a birnin tarayya Abuja.
Samuel ya bayyana cewa wannan shine Karo na biyu da ake debo ‘yan Najeriya cikin guda 150 da aka yi safarar su zuwa kasar ta Lebanon.
Ya kara da cewa za’a sauke mutanen a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, wanda kuma karo na farko da aka kwaso mutanen an sauke su ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad.
Bitrus ya kuma ce za’a killace ‘yan matan kafin daga bisani a sada su da iyalan su, don tabbatar basa dauke da cutar Corona.
You must be logged in to post a comment Login