Labarai
Mun fara amfani da jami’an farin kaya don dakile tarzoma a Kano- Bijilanti

Kungiyar bijilanti a jihar Kano ta ce, ta samar da jami’an farin kaya domin samun bayanan sirri na masu yunkurin tayar da zaune tsaye a lokacin zaben.
Shugaban kungiyar Shehu Muhammadu Rabi’u ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio
Tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne kan yadda kungiyar za ta bada tsaro a lokacin babban zaben kasar nan mai zuwa.
Wanda ya ce ‘sun shirya yin aiki tukuru a lokacin zabe domin dakile yunkurin ayyukan bata gari.’
Shugaban kungiyar bijilanti ta jihar Kano Shehu Muhammadu Rabi’u kenan a zantawarsa da Freedom Radio.
Rahoton: Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login