Labaran Wasanni
Mun gayyaci ‘yan wasan Kano huɗu zuwa tawagar ƙasa-Victor Nwanwe
Mai horar da tawagar ‘yan wasan ƙwallon ƙafa ta masu ƙafa ɗai ɗai (Amputee), ta Najeriya Victor Nwanwe , ya gayyaci ‘yan wasan tawagar jihar Kano shida zuwa babbar ƙungiya ta ƙasa don wakiltar ta.
Victor Nwanwe, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan Jaridu a birnin tarayya Abuja, biyo bayan kokarin da ‘yan wasan na jihar Kano sukayi a gasar masu buƙata ta musamman’ first National Para Games Abuja 2022′ karo na farko da aka kammala a Abuja.
“Duk da cewar muna da ƙalubale na kudadn gudanar ta tawagar hakan bai sa munyi ƙasa a gwiwa ba , saboda ƙwazo da himmar ‘yan wasan abun burgewa ne da azo a gani”.
” Ƙoƙarin ‘yan wasan Kano a wasan su karo na farko a gasar muka ga dacewar su da ƙwazon su na bugawa ƙasar mu wasa, don haka muka gayyaci mutum shida daga cikin su muna kuma kira ga Attajirai, Kamfanoni da gwamnatoci a dukkanin matakai da su shigo cikin wasan don bunƙasa shi” inji Victor Nwanwe.
A cikin ‘yan wasan na Kano da aka gayyata ƙarƙashin jagorancin masu horar da su , Rabiu Baita da El Ahmad Muhammad , sun haɗa da ..
Rabiu Yahaya sai Abba Musa da Yakubu Muhammad tare da Usman Ahmad sai Friday Hadu da Emmanuel Berthel.
Jihar Kano ta lashe lambar azurfa (Silver ), a gasar bayan da tazo ta biyu bayan rashin nasara da tayi a hannun jihar Kwara daci 1-0, a wasan ƙarshe.
You must be logged in to post a comment Login