Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun kaɗu da ficewar Abba Gida-gida – PDP

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta bayyana kaɗuwarta kan ficewar Engr. Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na Kano Bashir Sanata ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

Sanata ya ce, yanzu haka suna cikin alhini da takaici kan ficewar Abban daga jam’iyyar.

“Mutumin da ya samu ƙuri’u sama da miliyan guda, sannan a ce ya bar jam’iyyarka ai zai wahala a maye wannan giɓin”.

Ƙarin Labarai

Abin da ya sanya na fice daga PDP – Abba Gida-gida

Haryanzu Kwankwaso na nan a PDP-Bashir Sanata

Ya ci gaba da cewa “Muna kira ga sauran ƴan jam’iyyar da ke neman a rushe shugabanci su zo a haɗa kai domin a ciyar da jam’iyyar gaba”.

“Halin da ake ciki yanzu akwai takaici, har tsoron buɗe wayoyinmu muke domin saƙonnin da muke gani na yadda mutane masu amfani ke ficewa daga PDP” a cewarsa.

A ranar Lahadi ne Abba Kabir Yusuf wanda ya yiwa PDP takarar Gwamnan Kano a shekarar 2019 da wanda yayi masa mataki Aminu Abdussalam Gwarzo suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar.

Sun kuma bayyana shiga jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!