Labarai
Mun kama mai yiwa ‘yan Boko Haram safarar kwayoyin maye – NDLEA
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta samu nasarar kwato wasu kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram 19 a Jihar Lagos.
Ana zargin za a kai kwayoyin ga mayakan Boko Haram da ke jihar Borno.
Daraktan yada labaran hukumar Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Femi ya ce, kwayoyin na tramadol da diazepam sun kai guda dubu talatin da hudu da dari tara da 50.
Sanarwar ta ce an kama kwayoyin ne a hannun wani mai suna Muhammad Isah mai shekaru 25 a Agege, wanda ya ce wani ne mai suna Kakaki Abubakar ya ba shi don kai wa ‘yan Boko Haram a Maiduguri.
You must be logged in to post a comment Login