Labarai
Mun kama tabar wiwi a Kano – Ghali Sule
Kwamitin karta-kwana da gwamnatin Kano ta kafa don yaki da miyagun kwayoyi ya kama tabar wiwi da ya kai nauyin kilogram hamsin da uku da digo uku a Kano.
Shugaban kwamitin yaki da miyagun kwayoyi na jihar Kano Ghali Sule ne ya mika miyagun kwayoyin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, yau a nan Kano.
Ghali Sule wanda ya wakilci kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ce, sun kwace tabar wiwi ne wanda ake kokarin sayar da shi ga masu ta’ammali da miyagun kwayoyi anan jihar Kano.
Da ya ke mai da jawabi shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano, Dr. Ibrahim Abdul, ya yabawa kokarin kwamitin sakamakon hadin kan da suke basu wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
You must be logged in to post a comment Login