Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun kashe ‘yan Boko Haram a jihar Borno – Rundunar Operation lafiya Dole

Published

on

Dakarun Operation Lafiya Dole na rundunar sojojin kasar nan sun kashe ‘yan kungiyar ISWAP da Boko Haram guda takwas a jihar Borno.

Hakan na cikin wata sanarwar ce mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa Manjo Janar John Enenche.

Sanarwar ta ce bayaga mayakan na Boko Haram guda takwas wasu da dama sun tsere da munanan raunuka.

Ta cikin sanarwar dai manjo Janar John Enenche ya ce ‘yan kungiyar ta ISWAP sun kai hari ne wani sansanin soji da ke Kukawa a jihar Borno lamarin da sojojin su ka mai da musu martani.

Sai dai ya ce wasu sojoji guda uku sun rasa rayukansu sanadiyyar batakashin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!