Labaran Kano
Mun kwato bindigogi AK47 guda 18 a kasa da wata guda- CP Ibrahim Adamu Bakori

Rundunar Yan sandan jihar Kano, ta ce, a kasa da wata guda ta samu nasarar kama bindigogi kirar AK47 guda 18 daga hannun bata gari.
Kwamishinan yan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron wayar da kan Hakimai da Masu Unguwanni da Dagatai kan yadda za a magance matsalolin tsaro da magance shaye shayen miyagun kwayoyi.
Haka kuma kwamishinan, ya yaba wa kwamatin tsaro da gwamnatin Kano ta kafa bisa irin yadda su ke gudanar da aiki ba dare ba raba kuma kafada da kafada da sauran jami’an tsaro domin magance tu’ammali da miyagun kwayoyi.
You must be logged in to post a comment Login