Connect with us

Labarai

Mun saki sakamakon jarrabawar fiye da dalibai Miliyan 1 da dubu dari 2- JAMB

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta kasa JAMB ta ce zuwa yanzu ta saki sakamakon dalibai Miliyan daya da dubu dari biyu da sittin da hudu da dari tara da arba’in.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Fabian Benjamin ya fitar ga manema labarai a Abuja.

 

Ta cikin sanarwar, ya ce sakamakon ya kasance na daliban da suka zauna jarrabawar a ranakun Juma’a da Asabar ne.

 

Haka kuma, JAMB, ta bukaci daliban da suka rubuta jarrabawar da su bibiyi hanyar da ake bi don duba sakamakon nasu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!