Labarai
Kotun Koli ta sanya ranar ci gaba da sauraren karar dambarwar masarautar Kano

Kotun Kolin Najeriya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta sanya ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2027 domin ci gaba da sauraren karar da Alhaji Aminu Babba Dan agundi ya shigar inda ya ke kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara.
A zaman kotun na yau Litinin, lauyan mai kara, ya gabatar da rokon su kuma dukkanin lauyoyin da ke kare wadanda ake kara ba su yi suka ba amma shi lauyan majalisar dokokin Kano Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci, ya bukaci suka amma suka ce damar su ce.
Daga karshe kotun tadaga zaman zuwa shekara guda domin ci gaba da shari’ar.
Tun da farko dai Alhaji Aminu Babba Dan agundi ne ya shigar da kara inda ya ke kalubalantar matakim da majalisar dokokin Kano ta yi na cire Sarkin Kano Aminu Ado bayaro, inda hakan ta sa ya garzaya kotun tarayya da ke Kano domin nuna damuwarsa a matsayinsa na daya daga cikin masu nada Sarki, kotun kuma ta ce, ya na da hurumi.
Su kuma wadanda ya kai kara suka garzaya kotun daukaka kara ita kuma kotun ta ce bas hi da hurumin yin hakan, saboda haka ya garzaya kotun Koli domin ta tabbatar da hukuncin.
You must be logged in to post a comment Login