Labarai
Iran ta sha alwashin ɗaukar fansa kan ƙwace jirgin dakon kayanta da Amurka ta yi

Iran ta yi alƙawarin ɗaukar fansa bayan Amurka ta ƙwace wani jirgin dakon kayanta a Tekun gabas ta tsakiya.
Sojojin Amurka sun ce sun budewa jirgin wuta, lamarin da ya lalata injinsa, bayan ya yi ƙoƙarin wucewa ta shingen da Amurkar ta kafa.
Wakiliyar BBC ta ce shugaba Trump ya ce sojin ruwan Amurkar sun gargadi matuka jirgin da su dakata, amma suka yi kunnen kashi.
Wani kakakin sojojin Iran ya bayyana kwace jirgin a matsayin fashin teku, kuma saba yarjejeniyar zaman lafiyar da ke aiki.
You must be logged in to post a comment Login