Labarai
Mun samu nutsuwa sakamakon sakin daliban Tagina – UNICEF
Asusun tallafawa Ƙananan yara na Majalisar ɗinkin duniya UNICEF, ya ce ya samu nutsuwa bayan da masu garkuwa da mutane suka saki ɗaliban makarantar Salihu Tanko Islamiya da ke Tagina.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar a nan Kano Samuel Kaalu ya fitar a birinin Dutsen jihar Jigawa.
UNICEF ta ce tun bayan shafe tsawon kwanaki tamanin da takwas da daliban sukai a hannunsu masu garkuwa da mutane ba su samu nutuswa ba.
Hukumar ta bayyana takaicin ta kan yadda masu garkuwa da mutane suka mayar da makarantu wajen neman kudaden fansa ta hanyar yin garkuwa da ɗalibai.
Asusun UNICEF ya bukaci hukumomin da abin ya shafa dasu mayar da hankali wajen ganin sun samar da tsaro ga makarantun dake fadin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login