Labarai
Mun tanadi Manyan motoci 31 domin kwaso daliban daga Sudan- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta ce, manyan motoci 31 aka tanadar domin kwaso daliban da suka makale a Kasar Sudan, domin kai su kasar Masar inda za a dauko su a jiragen sama zuwa Nijeriya.
Babban Sakatare a ma’aikatar jin-kai ta kasa, kuma shugaban cibiyar da ke sanya ido kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki a kasar Sudan Dakta Nasir Sani Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wata ganawar sirri da manyan jami’an ma’aikatar a Abuja.
Ya ce, an samar da manyan motocin daukar fasinjoji 31, domin aikin kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan kuma an biya kowacce mota a kan Dala 30,000.
Haka kuma ya kara da cewa, jinkirin da aka samu a kan iyakar kasar Masar, ya samo asali ne sakamakon rashin biyan kudin da babban CBN ya yi a kan lokaci, tare da bukatar biyan kudin da gwamnatin Masar ta yi.
You must be logged in to post a comment Login