Connect with us

Coronavirus

Mun yiwa kusan mutane miliyan 4 rigaƙafin Corona – Gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce, an yi amfani da kaso tamanin da takwas cikin ɗari na kafatanin allurar rigaƙafin cutar corona guda miliyan huɗu da gwamnati ta karɓa a watannin baya.

 

Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko, Dr Faisal Shuaib, shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Abuja.

 

Ya ce, ya zuwa yanzu, an yiwa mutane miliyan uku da dubu ɗari huɗu da arbain da ɗaya da dubu ɗari ɗaya da arba’in da shida allurar rigaƙafin Oxford AstraZeneca.

 

A cewar sa, a kason farko an yiwa mutane miliyan biyu da dubu ɗari biyu da sittin da biyar da ɗari takwas da biyar, rigaƙafin yayin da aka yiwa mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya da saba’in da huɗu da ɗari uku da arba’in da ɗaya, allurar rigaƙafin kashi na biyu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!