Labarai
Mun zuba jarin Naira biliyan 120 a masaku da masana’antun jima – CBN
Babban Bankin Kasa (CBN) ya ce ya zuba jarin Naira biliyan120 a harkokin masaku da masana’antun jima da sarrafa auduga.
Mataimakin gwamnan bankin na CBN, Mista Edward Lamatek Adamu ne ya bayyana hakan a jiya, ya yin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin masana’antun sarrafa auduga a Abuja.
Bankin na CBN ya kuma ce a shekarar nan da muke ciki bankin yana kokarin noman auduga tan 300,000 don inganta masana’antun tufafi a kasar nan.
Mista Edward Adamu ya kara da cewa, kokarin da aka yi, ya haifar da karuwar masana’antun sarrafa tufafi a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login