Labarai
Muna baiwa manoma shawara su yi amfani da tallafi ta hanyar da ta dace – Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta bukaci manoman shinkafar da suka amfana da tallafin kayan noman da ta raba da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace, don kara bunkasa harkokin noma da kuma ciyar da kasar gaba.
Ministan Noma Muhammad Sabo Nanono ne ya bayyana hakan ta bakin mataimaki na musammam ga daraktar harkokin noma ta kasa Muhammad Shehu Adamu, yayin rabon tallafin ga kananan manoman shinkafa maza da mata su dari biyu a nan Kano.
Ya ce tallafin hadin gwiwa ne da gwamnatin kasar Japan, sakamakon yadda annobar cutar Corona da kuma ambaliyar ruwa suka taba manoman a bara.
A na ta jawabin mataimakiyar darakta mai kula da harkokin noman shinkafa Dr. Fatima Aliyu, cewa ta yi suna sa ran cigaba da ba da tallafin nan ba da jimawa ba.
Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa ko wane manomi ya amfana da buhu hudu na taki kamfa da buhu biyu na taki yuriya, sai buhu guda na irin shinkafa da lita goma ta maganin feshin ciyawa da galan daya na takin ruwa wato organic da kuma maganin kwari roba hudu.
You must be logged in to post a comment Login