Connect with us

Kiwon Lafiya

Muna buƙatar Buhari ya halarci ganawar da za mu yi da NMA – Ƙungiyar NARD

Published

on

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa NARD ta buƙaci shugaba Muhammadu Buhari da ya halarci ganawar da za su yi da ƙungiyar likitoci ta ƙasa NMA.

Mataimakin shugaban ƙungiyar Adejo Arome ne ya bayyana hakan, a zantawar sa da jaridar PUNCH.

Wannan ya biyo bayan ƙudurin ƙungiyar NARD na shigar da ƙara gaban kotun ɗa’ar ma’aikata, ƙarkashin jagorancin lauyan da ke kare haƙƙin ɗan adam na ƙasa Femi Falana.

Matakin na su na zuwa ne kwanaki biyu, bayan da ƙungiyar likitoci NMA ta gana da shugaba Muhammadu Buhari, inda ta buƙaci ƙungiyar NARD ta janye yajin aikin da ta shafe sama da wata guda tana gudanarwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!