Kiwon Lafiya
Muna dab da samar da cibiyoyin lafiya a matakin farko na zamani a jihohi 36 – Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce, ta kammala shirin ta na samar da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na zamani a jihohin ƙasar 36.
Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ƙaddamar da shugabannin kwamitin da za su kula da cibiyoyin lafiya a yankin kudu maso yammacin ƙasar nan.
Ehanire ya ce, cibiyoyin lafiya a matakin farko na zamani, za a samar musu da dukkanin kayan aiki na zamani, da ƙwararrun ma’aikata don su yi daidai da buƙata.
Ministan ya kuma ce, za a samar da su a yankuna mafi kusa da al’umma ta yadda za su taimaka wajen bada agajin gaggawa ga al’umma.
You must be logged in to post a comment Login