Kasuwanci
Muna kan Bakanmu na yajin aiki- Kungiyoyin kwadago

Kungiyar kwadago ta kasa NLC da takwararta ta TUC, sun bayyana cewa, suna nan a kan bakansu na ci gaba da yajin aiki yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan bukatunsu.
Kungiyoyin sun bayyana hakan ne ta cikin wani sako da suka wallafa a shafin X.
Sakon na kungiyoyin kwadago, ya kuma bayyana cewa, za a ci gaba da zama cikin yajin aikin har sai an kammala tattaunawar yau Talata da za a tsefe matsayar da aka cimma a daren jiya Litinin tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyoyin.
You must be logged in to post a comment Login