Labarai
Muna roƙon Ganduje ya samar mana da na’urorin UPS – Radio Kano

Gidan rediyon Kano ya nemi gwamnati ta samar masa na’urorin UPS domin ya ci gaba da gudanar da aikin sa a duk lokacin da aka ɗauke wuta kafin a kunna inji.
Shugaban gidan Rediyon Malam Ghali Sadik ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan da ya kare kasafin kuɗin baɗi na rediyon a majalisar dokokin Kano.
Wakilin mu Auwal Hassan Fagge ya rawaito Ghali Sadik na cewa, gwamna Ganduje ya samar musu da sabbin injinan wuta guda biyu.
A don haka yanzu na’urarorin UPS ɗin su ke buƙata domin ƙara inganta ayyukan su.
You must be logged in to post a comment Login